May 22, 2019 • 2M

BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.22

 
0:00
-1:40
Open in playerListen on);
HausaRadio.net - Online Hausa Radio

Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

Image result for BBC Hausa Safe

Host (mai gabatar da shirin): Fauziya Kabir Tukur (@fawzeyah)

 1. UK: Firam ministan Birtaniya, Theresa May, za ta gabatar da sabon shirinta na yarjejeniyar ficewar k'asar daga tarayyar Turai yau a gaban majalisa a k'ok'arin ganin yarjejeniyar ta samu karb'uwa.

 2. Nigeria: A Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta ce ba wani bane ya jefa k'asar cikin matsalar tsaron da ake fama da ita illa gwamnati karan kanta:

  "Kullun abin da ake gwadawa mutane cewa ainihin tashin hankalin bai kai yadda ake tsammani da she ba."

 3. An ce wai komai ya yi farko zai yi k'arshe. Shekara tara bayan fara fim d'innan mai dogon zango na k'asar Amirka, mai suna Game of Thrones da ya yi fice a fad'in duniya. An saki b'angaren k'arshe na shirin mai d'auke da abubuwan ban al'ajabi. Toh sai dai b'angaren ya dawo cece-kuce a tsakanin masu kallon shirin.

  "Na yi farin ciki da yadda aka k'are Brandon Stark shi ne ya cancanci ya hau kujerar mulki saboda shi kad'ai ya san tarihi."

  "Gaskiya dai ni, yadda ya k'are, ban ji dad'in haka ba ko kad'an. John Snow daga farko, na so a ce shi ne ya zamanto ya yi taken over iron throne d'innan."

 4. Toh ana cigaba da matsawa gwamnatin rik'en k'warya ta soji a Sudan kan ta sake komawa kan teburin shawara da jagororin masu zanga-zanga bayan tattaunawar ta samu tsaiko a ranar Talata.

Links:

 1. Full show (cikakken shirin): https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w3csyjr3

 2. Follow us <> Ku biyo mu @HausaRadio

Loading more posts…