BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.22

  
0:00
-1:40

Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

Image result for BBC Hausa Safe

Host (mai gabatar da shirin): Fauziya Kabir Tukur (@fawzeyah)

 1. UK: Firam ministan Birtaniya, Theresa May, za ta gabatar da sabon shirinta na yarjejeniyar ficewar k'asar daga tarayyar Turai yau a gaban majalisa a k'ok'arin ganin yarjejeniyar ta samu karb'uwa.

 2. Nigeria: A Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta ce ba wani bane ya jefa k'asar cikin matsalar tsaron da ake fama da ita illa gwamnati karan kanta:

  "Kullun abin da ake gwadawa mutane cewa ainihin tashin hankalin bai kai yadda ake tsammani da she ba."

 3. An ce wai komai ya yi farko zai yi k'arshe. Shekara tara bayan fara fim d'innan mai dogon zango na k'asar Amirka, mai suna Game of Thrones da ya yi fice a fad'in duniya. An saki b'angaren k'arshe na shirin mai d'auke da abubuwan ban al'ajabi. Toh sai dai b'angaren ya dawo cece-kuce a tsakanin masu kallon shirin.

  "Na yi farin ciki da yadda aka k'are Brandon Stark shi ne ya cancanci ya hau kujerar mulki saboda shi kad'ai ya san tarihi."

  "Gaskiya dai ni, yadda ya k'are, ban ji dad'in haka ba ko kad'an. John Snow daga farko, na so a ce shi ne ya zamanto ya yi taken over iron throne d'innan."

 4. Toh ana cigaba da matsawa gwamnatin rik'en k'warya ta soji a Sudan kan ta sake komawa kan teburin shawara da jagororin masu zanga-zanga bayan tattaunawar ta samu tsaiko a ranar Talata.

Links:

 1. Full show (cikakken shirin): https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w3csyjr3

 2. Follow us <> Ku biyo mu @HausaRadio

RFI Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin 07h00 Asabar 2019.05.18

  
0:00
-1:16

VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

  
0:00
-1:50

Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

Image result for voa hausa safe

Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri

 1. US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka.

 2. US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya.

 3. Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kafa wata had'akar yak'i da ayyukan ta'addaci kamar irin wadanda aka kafa su a k'asashen Iran da Afghanistan domin yak'i a yankin Sahel.

 4. Nigeria: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dad'in dangantaka da shugabannin majalisar dokokin k'asar a wa'adin mulkin sa na farko, da ya ce ya kawo cikas a harkokin mulki. Sai dai masu kula da lamura suna cewa wannan shi ne demokradiya.

  “Ai aikin majalisa, d'aya daga cikin manya-manyar ayyukan shi ne ta taka birki ga b'angaren zartasuwa. Kuma duk wanda ya ke taka maka birki, ba lalle bane a ce ra'ayinku yana tafiya dai-dai kuma ana samun jittuwa a ko wane lokaci.”

 5. Taraba: Muna kuma da rahoto kan cigaba da jami'an tsaro suke samu a jihar Taraba a yunk'urin shawo kan masu garkuwa da jama'a.

 6. Sai kuma shirin Lafiya Uwar Jiki da Hauwa Umar ke gabatarwa.

Links:

 1. Stream or download: https://www.voahausa.com/a/4901612.html

 2. Permalinks: http://bit.ly/VOAHausaSafe20190517

 3. Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

 4. Tweet:

BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

  
0:00
-1:34

Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

Image result for BBC Hausa Safe

Host <> Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa

 1. Yau ce dai ranar yak'i da cutar hawan jiniwato hypertensionta duniyaToh ko ya mutum zai kare kansa daga kamuwa da wannan cuta?

  "Farko, mutum ya zama cewa yana yawan motsa jiki. Sannan kuma a daina yawan cin abinci da tsike, kamar na turawa na gwangwani. Sannan kuma mutum ya dinga cin abinci wanda ake bada shawara a ci kamar 'balance diet.' Sannan kuma ya zama cewa mutum yana samun isasshen hutu, yana samun isashen bacci."

  Related tweet, article:

 2. A yau zamu cigaba da kawo muku hirar da BBC ta yi da jarumin fina-finan Kannywood, wato Adam A. Zango. Inda har ma a cikin hirar ta sa, ya d'auki wani alk'awari:

  “Na yi alk'awarin cewa, abinda aka min gori, 'ya'ya na, ba za ayi musu ba inshaAllahu. Sannan abin da aka min gori, daga yanzu zuwa lokaci kad'an, bi'iznillahi, babu wanda zai k'ara bud'a baki ya min gori akai.”

  Related:

 3. A Najeriya, hukumar zab'e mai zaman kanta ta k'asar ta sanya lokacin da za a gudanar da zab'en gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa.

 4. Sannan wata tawagar masu bincike, ta yi kiran da wajibta yin riga kafin cutar k'yanda ga dukkan yaran da za su fara karatu a matakin primary.

List to the full program below <> A saurari cikakken shirin a :

 1. Stream: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w3csyjj9

 2. Download: https://drive.google.com/open?id=10qc4fTkj5_KZi_UiWsP4_v0aMef6ftG3

 3. Permalink: http://bit.ly/BBCHausaSafe20190517

 4. Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

 5. Tweet:

Loading more posts…