Hausa Newsletter
Hausa Newsletter
Kanun Labaran BBC Hausa (News Headlines) na 20250509
0:00
-5:27

Kanun Labaran BBC Hausa (News Headlines) na 20250509

Kanun Labaran BBC Hausa na 8-9 Mayu 2025 https://youtu.be/lRvynmNLCok

00:00-01:30 Kanun Labaran BBC Hausa - Shirin Yamma na 8 Mayu 2025
🎧 Cikakken sautin shirin: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/programmes/p030s4mx

✝️ 🗳️ An zaɓi Robert Prevost a matsayin sabon Fafaroma inda ya zame ba'amurke na farko da ya jagoranci cocin Katolika. To ko ya mabiya ɗarikar katolika su ka ji da wannan zaɓe?

"Ina farin ciki don mun sami sabon Fafaroma Leo na goma sha hudu (XIV/14th). Muna fatan alheri ga ikilisiya mai tsarki Katolika."

"Na yi murna saboda Pope Leo mai fourteen da an zaba yau. Muna mashe fatan alheri."

🇳🇬 ✋🏾A Nigeria, gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar, ta lashe takobin ganin an hukunta duk mutanen da aka kama da laifin yinwa ta yarinya 'yar shekara goma sha shida (16) fyaɗe a garin Likoro.

"Dukkansu sun yi fyaɗe da ita. Wasu ta ƙarfi, wasu ta yaudara a bata ɗari biyu (₦200) ko ɗari biyar (₦500) wasu kuma su bi ta har ɗakin mahaifiyanta, mahaifiyan makauniya, mahaifin makaho, ita ma idan ta ɗaya."

🇳🇬 🎙️ Har wa yau dai a Najeriyar, Gwamnatun jihar Kano ta fitar da sanarwar haɗin guiwa da shugabannin kafafen watsa labarai inda aka dakatar da gabatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye.

1:32-2:59 Kanun Labaran BBC Hausa - Shirin Safe na 9 Mayu 2025 🎧 Cikakken sautin shirin: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w3ct7tvt

✝️ 🙏 A cikin shirin za ku ji nan gaba a yau ne sabon Fafaroma zai halarci taron addu'o'i tare da limaman Fadar Vatican.

🇷🇺 🥁 Can a Rasha kuwa, ana shirin faretin soji na tinawa da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu (WW2).

🇳🇬 🗳️ Idan muka je Nigeria, jam'iyyar APC mai mulki ta ce ko a jikinta kan gwamnatin je ka nayi ka da 'yan adawar ƙasar suka kafa.

"Adawa ce wacce ba ta yin tasiri. Iya dai kawai cikowa, su yi ƙorafi ko su faɗi wasu abubuwa dai na tattaunawa a gaba da abin da gwamnati ke yi. Amma ba wani abu ba ne na tā da hankali ko na kawo firgici ko wani abu."

🇳🇬 ⛽︎ Aiwayo a Najeriyar, yayin da ake ci gaba da damuwa kan cire tallafin man fetur, Ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ta ce tuntuni ya kamata a cire wannan tallafi.

"Ba ɗaya ba, ba biyu ba, ai ake ta maganun cewa ya kamata cewa to a cire. Kuma to amma ta wane mataki da za a cire? Amma da aka kai ga matuƙa an ce wai ƙarshen tika tika tik aka kai ga tik. Yanzu ai an cire shi ko."

3:00-4:09 Kanun Labaran BBC Hausa - Shirin Hantsi na 9 Mayu 2025
🎧 Cikakken sautin shirin: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w17304ftv4jvq7v

🇮🇳 🇵🇰 India da Pakistan na ci gaba da zargin juna kan ƙaruwan tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu.

🇮🇱 💣 Isra'ila ta ce an kashe sojojin ta biyu a gwabzawar da suka yi da mayaƙan Hamas a kuduncin Zirin Gaza.

🇳🇬 🍅 Manoma tumatar a Nigeria kuwa na ci gaba da bayyanar asarar da suke tabka sakamansu kwan tsutsar Ebola da ke lalata musu tumatar.

"Ya ja ma manoma mummunar asara. Wadda ta durƙusa da yawancin duk manoman tumatar da suka yi numa a wannan shekarar. Wani filfillo ne wanda yake yaɗuwa cikin sauri. A jihar Katsina a ƙalla manoma sun yi asarar abinda ya kai biliyan uku (₦3b)."

🇪🇺 ⚽️ A fagen wasanni kuwa za ku ji Manchester United da Tottenham sun kai wasan ƙarshe a gasar zakarin turai ta Europa League.

"Gaskiya muna cikin farin ciki sosai, mu 'yan Manchester United. Haka muke fata Allah ya ba mu nasara a kan Tottenham a wasan da za mu yi na ƙarshe."

4:11 Kanun Labaran Shirin Rana na 9 Mayu 2025
🎧 Cikakken sautin shirin: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/programmes/p030s4mp

✝️ ⛪︎ Fafaroma Leo na goma sha huɗu ya gabatar da huɗubarsa ta farko a matsayin jagorar cocin Katolika.

🇵🇰 🇮🇳 Ma'aikatar harkokin wajen India ta zargi Pakistan da amfani da jiragen saman passenger a matsayin garkuwa a rikicin da ƙasashen biyu ke yi a kan iyakarsu.

🇳🇬 🕋 A Nigeria, a yau Juma'a ne ake sa ran tawagar farko ta wani ta yi aikin hajjin bana za ta tashi daga binnin Owerri na jihar Imo.

🇳🇬 ䷯ Har wa yau dai a Nijeriyar, gwamnatin jihar Kano ta ce jami'an hukumar DSS sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da kisan wata ƙaramar yarinya a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

"Wannan yarinya, waɗannan mutanen ne suka ɗauke ta suka ɓoye kuma suka nemi kudin fansa. Amma kafin a danga musu kudin fansar, kuma sun riga sun hallaka wannan yarinyar, suka jefa ta cikin wata tsohuwar rijiya, wadda babu ruwa a cikinta. Suka jefa gawarta."

Discussion about this episode

User's avatar