VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

  
0:00
-1:50

Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

Image result for voa hausa safe

Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri

 1. US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka.

 2. US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya.

 3. Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kafa wata had'akar yak'i da ayyukan ta'addaci kamar irin wadanda aka kafa su a k'asashen Iran da Afghanistan domin yak'i a yankin Sahel.

 4. Nigeria: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dad'in dangantaka da shugabannin majalisar dokokin k'asar a wa'adin mulkin sa na farko, da ya ce ya kawo cikas a harkokin mulki. Sai dai masu kula da lamura suna cewa wannan shi ne demokradiya.

  “Ai aikin majalisa, d'aya daga cikin manya-manyar ayyukan shi ne ta taka birki ga b'angaren zartasuwa. Kuma duk wanda ya ke taka maka birki, ba lalle bane a ce ra'ayinku yana tafiya dai-dai kuma ana samun jittuwa a ko wane lokaci.”

 5. Taraba: Muna kuma da rahoto kan cigaba da jami'an tsaro suke samu a jihar Taraba a yunk'urin shawo kan masu garkuwa da jama'a.

 6. Sai kuma shirin Lafiya Uwar Jiki da Hauwa Umar ke gabatarwa.

Links:

 1. Stream or download: https://www.voahausa.com/a/4901612.html

 2. Permalinks: http://bit.ly/VOAHausaSafe20190517

 3. Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

 4. Tweet: